Yaiwa yarinya yar shekara 10 fyàdé bayan ba ta lemu mai dauke da sinadarin saka maye.
Wani matashi mai shekara 33 a duniya, ana zarginsa da yin amfani da sinadarin da ke sanya maye wajen gusar da hankalin wata karamar yarinya ‘yar shekara 10, tare da yi mata fyade a karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.
Matashin wanda ya yaudari yarinyar ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin da ke sanya maye domin samun damar lalata da ita ba tare da saninta ba.
A cewar wata sanarwar manema labarai da kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, wanda ake zargin ya samu damar fyade da yarinyar ne ta hanyar amfani da karfin tsiya.
Ya ce, “A ranar 25 ga watan Mayun 2023, wani mutum da ke kauyen Nasaru a karamar hukumar Ningi ya kai rahoto caji ofis din ‘yan sandan Ningi, inda ya ce wani matashi da suke gari daya ya yaudari ‘yarsa mai shekara 10 ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin da ke sanya maye wanda hakan ya sanya hankalinta ya gushe.
“Ya yi amfani da wannan damar ya yi mata fyade, wanda ya hakan ya sanya yariyar ta gamu da raunuka a al’aurarta kana ta yi ta zubar da jini.”
A wani Rahoto sanarwar, tun lokacin da suka amshi rahoton, tawagarsu cikin hanzari suka garzaya inda lamarin ya faru tare da daukar yarinyar zuwa babban asibitin Ningi daga bisani aka sauya mata wurin jinya zuwa asibitin kula da masu yoyon fitsari (NOFIC) da ke Ningi, bayan kaurin jikinta aka sake nausawa da ita zuwa asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa domin neman kulawar likitoci.
A cewar Wakil, tun lokacin ‘yan sanda suka sha alwashin sai sun cafko wanda ya aikata hakan domin tabbatar da yarinyar ta samu adalcin da ya dace ta samu, “Kan hakan mun cafke wanda ake zargi, Danladi Ibrahim.
“A lokacin da ake tuhumarsa, ya amsa da kansa cewa ya aikata laifin, don haka bincike na cigaba da guduna da zarar aka kammala za mu gurfanar da shi a gaban kuliya.”
Daga bisani rundunar ‘yansandan ta jawo hankalin al’umma da cewa su rika sanya ido da lura da yankunansu domin dakile aniyar bata gari a kowani lokaci tare da gaggawar kai rahoton faruwar lamuran da ba daidai ba cikin hanzari domin daukan matakan gaggawa.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim