‘Yan Bindiga da Masu garkuwa da mutane Sun tafi Yajin aiki- Minista Kwadugo, Ngige.
Minstan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya bayyana karancin naira da cewa, shima yana da nashi muhimmancin.
Ministan wanda yayi wannan jawabin a ranar laraba, a wani shiri gidan talabijin mai suna “Politics Today”.
Ya yi musun cewa, akwai matukar amfani da najeriya zata amfana dashi, a cikin wannan yanayin.
Dan haka Ngige ya fahimci cewa, yanayin da ya kema al’ummar najeriya ciwo ya kasance mafi ga wani yanayin.
Kamar yadda yace, shin ko wannan yanayin na karancin kudi a hannun jama’a yana da amfani. Ko dai yana da amfani ko baya da amfani? Amma tsarine mai kyau.
Amma yanayin yazo da wani ciwo ga ‘yan najeriya, amma kuma akwai alfanu a ciki, Na farko dai mutane basu siya kuri’u ba, a lokacin Zabe.
Ina yawan zuwa wurin zabe, kuma ni nasan Abubuwan da nake gani, Kwata kwata ba Musayar kudi ga masu kada kuri’a, a Zaben.
Kwata kwata wannan ba Abu bane mai sauki, Masu garkuwa da mutane sun tafi Hutu., Masu garkuwa da mutane sun tafi yajin Aiki, kamar yadda ‘yan ta’adda Sun tafi Hutu.
A yayin da yake magana akan yajin aikin NLC yace, bankuna sun saki kudi a cikin kasar.
Sun saki kudi ga ‘yan najeriya, kuma matsalar kudi a najeriya ta kusa zuwa karshe kwa nan nan.
Dalilin rashin kudi a hannun jama’a an samu saukin masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
A dalilin yajin aikin da NLC ta tafi bankuna sun fara sakin kudi ga ‘yan najeriya.
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.