Yan bindiga sun kaiwa zababben Dan Majalisar dokokin jihar Binuwe Mummunar hari.
Zababben dan majalisar dokokin jihar Benue mai wakiltar mazabar Gboko-Yamma, Mista Aondona Dajoh ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi.
A cewar rahoton, ‘yan bindiga sun yi masa kwanton bauna ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida a daren ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, a mahadar Gyado da ke karamar hukumar Gboko a jihar. Ya yi nasarar tserewa amma maharan sun kona motarsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Binuwai, SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.
‘Yan bindiga sun kai wa zababben dan majalisar dokokin jihar Benuwe mai wakiltar mazabar Gboko West Hon. Hyacinth Aondona Dajoh hari a daren jiya tare da kona motarsa a Gboko.
A rahoton ya cigaba da cewa; Zababben dan Majalisar ya tsallake rijiya da baya, inda ya kubuta daga wanna gadon zare da maharan suka kai masa.