Yan Bindiga Sun Kashe Sarakunan Gargajiya Da Wani Dan Kasuwa A Jihar Bauchi.
Wasu da ake zargin miyagun ‘yan bindiga ne sun shiga karamar hukumar Ningin jihar Bauchi, su ka yi gaba da Hakiman wasu garuruwa.
Premium Times ta ce Sarakan da aka dauke su ne na Bakutunbe da Balma, ana zargin an yi garkwa da su a ranar Asabar, ana neman kudin fansa.
Baya ga Sarakan da su ka fada hannun ‘yan bindigan, sun kuma kashe wani shahararren ‘dan kasuwar yankin da aka fi sani da Haruna Dan-Oc.
Wani mazaunin garin da ya boye sunansa saboda barazanar tsaro ya shaida cewa gungunan miyagun sun auko Balma ne da karfe 11:00 na dare.
A cewarsa ‘yan bindigan sun buda wuta kafin su dauke Hakimin garin, su yi awon gaba da shi.
Bayan ‘yan bindigan sun tsere aka tsinci gawar Dan OC a kwance a kasa da harsashi a cikin kansa, ko da aka je babban asibitin Ningi, sai aka ce ya mutu.
Rahoto ya ce a daren ne kuma wadannan miyagun ‘yan ta’adda su ka shiga Bakutunbe, su ka dauke mai garin kauyen, Ya’u Gandu mai shekara 45.
‘Yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan takwas domin a iya karbar fansar kowane daga cikin wadannan Bayin Allah da aka yi garkuwa da su.
Shugaban karamar hukumar Ningi ya ce zai kyau a aiko masu da sojoji domin su kare al’umma, tare da kira ga mazauna yankin su dage da addu’o’i.
An nemi jin ta bakin Muhammed Wakili wanda shi ne Kakakin Rundunar ‘yan sandan Bauchi, amma ba ayi nasarar samun wayoyin salulansa ba.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim