‘
Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da akalla masu ibada uku a wani masallaci da ke Ughelli a jihar Delta da safiyar Juma’a, kamar yadda wani mazaunin garin ya bayyana.
An ce an jikkata masu ibada 11 a harin wanda ya sa mazauna yankin cikin fargaba.
Wani mazaunin garin da ya zanta da kamfanin Dillincin labarai ta Najeriya (NAN) ta wayar tarho, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 6.47 na safe a lokacin da wasu musulmi suke gudanar da sallar asuba a babban masallacin Juma’a, dake kan titin Okoroda a Ughelli.
Mutumin wanda ya bayyana sunansa da Larry, ya ce da yawa daga cikin mazauna garin sun barke da barci sakamakon harbe-harbe da kuma kuka mai karfi daga mutanen da ke cikin masallacin.
“Sunana Larry, ni direban abin hawa ne a nan Ughelli. Ina zaune kusa da babban masallacin, don haka da safiyar yau da misalin karfe 6:45 na safe sai muka ji harbi a masallacin. Saboda tsoro, mutane da yawa a harabar gidana sun firgita kuma mun zauna a ciki muna leƙen tagogi ne kawai.”
“Yayin da harbin ya ci gaba, mun ji kuka mai karfi daga wasu masu ibada a cikin masallacin,” in ji Larry.
A cewarsa, bayan da maharan suka fita, da yawan mazauna garin sun yi dafifi zuwa masallacin domin ganin abin da ya faru.
Ya ce mazauna yankin sun taimaka wajen kwashe wadanda suka jikkata, ya kuma ce wadanda suka tsira daga harin sun samu munanan raunuka.
Larry ya ce wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun shaida wa mazauna garin cewa ‘yan bindigar sun tafi da wasu ’yan uwansu guda uku.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar wa NAN harin, sai dai ya ce masallata 11 ne kawai suka jikkata a harin. Sai dai bai tabbatar da sace wasu masu ibada uku ba.
“Na kira DPO a Ughelli, ya tabbatar min da cewa mutane 11 sun jikkata a harin da aka kai a masallacin.
“Duk da haka, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin kuma za mu sanar da ku yayin da muke kokarin bankado masu laifin.
Edafe ya ce “A yanzu ba a kama su ba amma ina mai tabbatar muku da cewa za mu shiga cikin lamarin.”
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida