Yan bindiga sun lalata kayan zabe a Taraba .
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun lalata kayayyakin zabe a unguwannin Akete Asibiti da ke karamar hukumar Donga a jihar Taraba.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa Donga gidan dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Sanata Emmanuel Bwacha ne. Haka kuma an yi imanin cewa unguwannin Akate da Asibiti sun kasance tungar jam’iyyar adawa ta APC.
Dattijo James Chimin, wani mazaunin unguwar wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki hedikwatar gundumar ne da misalin karfe 6:30 na safe a daidai lokacin da jami’an INEC ke shirin kwashe kayan zaben zuwa rumfunan zabe daban-daban, inda suka fara harbe-harbe kai tsaye. .
A halin da ake ciki dai an nuna rashin jin dadin masu zabe a karamar hukumar Wukari mahaifar dan takarar gwamnan PDP kamar yadda wakilinmu ya sanyawa ido.
Wasu daga cikin masu kada kuri’a da suka zanta da wakilinmu a Wukari, sun ce akwai damuwa game da tsaron masu kada kuri’a.
A halin da ake ciki, dan takarar gwamnan PDP Col. Kefas Agbu ya yaba da wannan tsari ya zuwa yanzu.
Agbu wanda ya yi magana bayan ya kada kuri’arsa a makarantar firamare ta Ebeneza ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa za a gudanar da atisayen cikin lumana duk da faruwar lamarin a unguwannin Akate da Asibiti na Dongo, ya kuma yi kira ga masu kada kuri’a da su kasance cikin tsari domin samun nasarar aikin.
RAHOTO -ZUBAIDA ALI TARABA