Yan bindiga sunkai hari babban Ofishin INEC A Enugu
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) a karamar hukumar Enugu ta Kudu a jihar Enugu.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:12 na daren Lahadi, ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda yayin da daya kuma ya samu raunuka kuma yanzu haka yana karbar magani.
INEC a cikin wata sanarwa da ta raba wa LEADERSHIP a Abuja ranar Litinin mai dauke da sa hannun kwamishinanta na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ta ce an ruguza kofar jami’an tsaro na cibiyar.
Yayi sa’a, Okoye ya ce maharan ba su iya shiga babban ginin ba sakamakon daukin gaggawar da jami’an ‘yan sanda da na sojoji daga shiyya ta 82, Enugu suka yi.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar da kuma jami’an hukumar REC da kan su suna wurin nan take suka samu labarin harin. A cikin ‘yan sandan biyu da aka tura domin kare wurin, daya daga cikinsu ya rasa ransa yayin da daya ya samu raunuka kuma yana samun kulawa. Hukumar ta yi addu’ar Allah ya jikan dan sandan da ya rasu, ya kuma baiwa wadanda suka jikkata cikin gaggawa.” Inji shi.
Ya ce kwamishinan zabe na jihar Enugu, Dr. Chukwuemeka Chukwu ne ya kai rahoton harin ga hedikwatar hukumar.
Ya ce, “Hukumomin tsaro na binciken lamarin. Bugu da kari, an kira taron kwamitin tuntuba tsakanin hukumomi kan harkokin tsaro (ICCES) a jihar Enugu wanda hukumar ta REC da kwamishinan ‘yan sanda suka jagoranta domin tattauna sabon afkuwar lamarin tare da tsara wasu dabaru na kayyade ofisoshin da kuma ba da kariya ga jami’an tsaro. ma’aikata da kayan aiki.”
Ya kara da cewa za a sake gina kofar gidan da aka lalata, kuma hukumar na ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 a jihar Enugu da ma kasar baki daya kamar yadda aka tsara.
RAHOTO -ALIYU SHU’AIBU ALIYU (MARIRI)