‘Yan fashi sun kashe direbobi uku, sun sayar da abin hawa ga wani kamfanin kasar China
Wani da ake zargin dan fashi da makami, Williams Abiodun, a ranar Laraba ya bayyana yadda ‘yan kungiyarsa suka kashe wasu tare da sayar da motocinsu a Benin, jihar Edo.
Abiodun, yayin da ake gabatar da shi tare da wasu mutane 10 da ake tuhuma a hedikwatar rundunar da ke jihar Edo, ya ce shi da wasu ’yan kungiyarsa guda hudu kan yi kama da ma’aikatan wurin ne don jawo direbobin da ba su ji ba, inda suke yi musu fashin motocinsu.
Ya ce, “Idan muka isa wurin, mukan tattara motocinsu, muna kashe su tare da sayar da motocinsu.
“Mun kashe mutum na farko, muka tattara motarsa muka sayar wa wani kamfanin kasar Sin, Mutum na biyu ma’aikacin babur ne wanda muka kashe muka sayar da babur dinsa.
Amma an kama mu ne a lokacin da muke kokarin sayar da wata mota kirar Toyota Sienna da muka samu a samamen na uku.”
Dan kungiyar Abiodun Akin Amadin, ya ce ya samu Naira 90,000 a yayin gudanar da ayyukan.
Ya ce, “Abiodun ya gaya mani cewa aikina shi ne na sa ido in ga wanda ke zuwa, Na farko da muka yi, ya ba ni Naira 35,000; Na samu Naira 55,000 a aiki na biyu kuma an kama mu a lokacin da muke kokarin sayar da mota ta uku Mun kashe mutane uku baki daya.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Dankwara, a yayin faretin, ya ce an kama mutane 135 da ake zargi da aikata laifuka tun bayan hawansa ofis a jihar, ya kuma kara da cewa ‘yan sandan sun kwato N1.2m da nagartattun makamai da harsasai daga hannun wadanda ake zargin.