Yan Sanda Sun Damke matashi Mai Shekaru 17 da laifin Dirkawa Mata su goma Ciki a Ribas.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta bayyana yadda jami’anta suka yi nasarar cafke wasu da ake zargi da samarwa tare da siyar da jinjiraye.
An ruwaito yadda aka kama wadanda ake zargin ranar Talata a wurare daban-daban tsakanin Obia zuwa Akpor da karamar hukumar Ikwerre
Jami’an sun ceto yara mata 10 dauke da juna biyu, sannan an gano yadda idan an haifi yaran ake ba kowaccensu N500,000 sannan a siyar da jinjirayen
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas a ranar Talata ta bayyana yadda jami’anta suka cafke wani yaro mai shekaru 17, Noble Uzuchi da Chigozie Ogbonna, mai shekaru 29 da suke aikin yi wa mata ciki a wani guri da aka haifa gami da siyar da jinjiraye.
An ruwaito yadda hudun da ake zargi suke cin karensu ba babbaka tsakanin Obia zuwa Akpor da karamar hukumar Ikwerre na jihar.
Har ila yau, ‘yan sandan sun labarta yadda suka ceto yara mata 10 masu juna biyu.
Kakakin ‘yan sandan, Grace Iringe-Koko, a wata takarda data fita a Port-Harcourt ranar Talata, ta ce an yi nasarar kamasu ne bayan samun labari, wanda rundunar tayi amfani da shi.
Kamar yadda takardar ta bayyana a ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, misalin karfe 4:45 na yamma, yayin amfani da wani bayanin sirri da rundunar ‘yan sandan jihar Ribas suka samu, jami’an binciken sirri na sashin C41 sun kai samame daban-daban gidaje biyu a Igwuruta da yankin Omagwa. Inda ake boye yaran da ake safara.”
‘Yan sandan sun ce masu harkallar suna hayar Uzuchi da Ogbonna don yin lalata da yara mata gami da dirka musu ciki.
“Wadanda jami’an suka ceto guda 10 ne, kusan dukkansu na dauke da juna biyu..”
Iringe-Koko, babban jami’in ‘yan sandan yankin, ya ce bincike ya bayyana yadda idan aka haifi ‘jinjiri ta harkallar, shugaban sabgar sai ya aje jinjirin gami da biyanta N500,000.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ta bayyana yadda aka haifi wasu jinjiraye kwanakin baya, sannan aka siyar dasu.
A cewarta duk wadanda lamarin ya auku dasu sun fallasa yadda aka yaudaresu da sai da yaran saboda matsanancinyar bukatar kudi da suke. An gano wata mota kirar Honda Pilot Jeed, launin fara a wurin shugabar harkallar.
“An mayar da lamarin sashin binciken laifuka na jihar, sannan ana kokarin bincikowa tare da kamo wadanda suke siyan jinjirayen.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim