‘Yan sanda sun kama mutane 405 da ake zargi da fashi da makami, Tare da kashe 51
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce an kama mutane aƙallan 405 da ake zargi da aikata fashi da makami tare da kashe wasu 51 a wata musayar wuta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya alƙaluman yayin da yake magana kan nasarorin da rundunar ta samu.
Hundeyin ya ce an kama mutane 245 da ake zargi, 25 kuma aka kashe a cikin 17 na fashi da makami a shekarar 2021, yayin da aka kama 160 sannan an kashe 26 daga cikin 20 da suka faru a shekarar 2022.
Ya ce an daƙile ayyukan fashi guda 350 a cikin lokacin da ake nazari, inda 169 a shekarar 2021 da 181 a shekarar 2022.
Kakakin ya ce an ƙwato makamai 206 da alburusai 775 a cikin wannan lokacin, tare da rubuta makamai 108 da alburusai 348 a shekarar 2021, yayin da aka kwato makamai 98 da alburusai 427 a shekarar 2022.
Hundeyin ya ce an kama mutane 262 da ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne a cikin wannan lokaci daga cikin ƙararraki 32 da aka samu, yayin da 128 aka kama daga cikin 18 a shekarar 2021, wasu 134 daga cikin ƙararraki 14 a shekarar 2022.
‘Yan sandan Legas sun gurfanar da wani mutum a gaban kuliya bisa zargin zamba N7m
Ya ƙara da cewa, a shekarar 2022 an samu laifukan kisan kai guda 206 a kan 192 a shekarar 2021, inda ya kara da cewa wadanda suka kashe kansu sun tashi daga 25 a shekarar 2021 zuwa 30 a shekarar 2022.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda uku ne suka rasa rayukansu a cikin rundunar ‘yan sandan daga hare-hare 20 a tsawon lokacin, inda a kowace shekara ana samun hare-hare 10.
Ya ce an rage yawan masu garkuwa da mutane daga biyar a shekarar 2021 zuwa biyu a shekarar 2022, tare da kama mutane uku da ake zargi.
Hundeyin ya ce an kwato motoci 35 a cikin wannan lokaci inda 10 a shekarar 2021 da 25 a shekarar 2022.
Ya ce har yanzu ba a gano sauran motoci 32 da aka sace da aka kai wa rundunar ba.
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba Shanga.