Yan sanda sun kashe mai Garkuwa Da Mutane tare da ceto wadanda ke hannunsa a Adamawa
‘Yan sandan Adamawa Sun Kashe Mai Garkuwa da Mutane, sun Ceto Wadanda akayi Garkuwa da su
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun ceto wasu fastoci da aka yi garkuwa da su daga maboyar masu garkuwa da mutane a tsaunin Gujubabu da ke karamar hukumar Yola ta Kudu. Rundunar ‘yan sandan ta kuma kashe daya daga cikin wadanda ake zargin.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya sanya wa hannu, kuma ya wallafa a shafin sa na Twitter na rundunar a ranar Juma’a.
Rundunar ta kuma bayyana cewa kayayyakin da aka kwato a yayin aikin sun hada da bindiga kirar Ak-47 guda daya, wayoyin hannu, da sarka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bugu da kari a kan kudurin rundunar na inganta dabarun da suka dace, rundunar a ranar 26/5/2023 ta katse wata kafar sadarwar da ta hada wani bangare na Gujubabu, Bole, Yolde Pate da kuma wani bangare na Yadim, a kananan hukumomin Yola ta Kudu da Fufore.
“Aikin wanda jami’an rundunar a karkashin jagorancin Kwamanda Crack Squad suka gudanar tare da hadin guiwar mafarauta na Tabital Pulaku, sun samu sakamako mai kyau.
“Sakamakon nasarorin da aka samu ya biyo bayan dabarun hadin gwiwa tare da Mafarauta don tarwatsa maboyar laifuffuka da hukumar ta tsara don kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su tare da kama masu laifin. Wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, bayan da suka ga mutanenmu a kusa da maboyar, sai suka hada su da bindiga. Sakamakon haka an kashe daya daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harsashi.
“Abin sha’awa, an kwato bindiga kirar AK-47 guda daya tare da harsashi guda ashirin da biyar sannan kuma an ceto wadanda abin ya shafa ba tare da wani rauni ba.”
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.