Yan Sanda Sun Mayar Da Motocin Matawalle Bisa Umarnin Kotu.
‘Yan Sanda Sun Bi Umarnin Kotu, Sun Mayar Da Motocin Tsohon Gwamnan Zamfara, Matawalle.
Rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara ta mayar da dukkan motocin da aka dauka daga gidan tsohon gwamnan jahar, Bello Matawalle a jahar.
A ranar 10 ga watan Yuni ne jami’an ‘yan sanda suka kama motoci 40 a wani samame da suka kai gidajen tsohon gwamnan na Gusau da kuma garin Maradun.
Sai dai mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu na babbar kotun tarayya da ke Gusau a hukuncin da ya yanke a ranar 15 ga watan Yuni ya umarci dukkanin hukumomin tsaro da suka kwashe motocin da su mayar da su gidajen Matawalle cikin sa’o’i 48.
Alkalin wanda ya bayar da umarnin a karar da tsohon gwamnan ya shigar, ya kuma hana sufeto-janar na ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sandan jahar Zamfara daukar wani mataki kan lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, Yazid Abubakar, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar a Gusau. Ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin kotu.
Abubakar ya ce: “Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.
Mun mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya da ke Gusau, kamar yadda nake magana da ku a yanzu, babu wata mota guda da ke hannun ‘yan sanda.