Yanda aka kama wani matashi, a yakin da ya ke ƙokari sace janareton kotu a jihar Ogun.
An kama wani matashi dan shekara 28 mai suna Folorunsho Olaniyan a lokacin da yake kokarin sace janareta mallakar wata kotun al’ada a karamar hukumar Ado-Odo Ota ta jihar Ogun.
PUNCH Metro ta tattaro cewa Olaniyan, dan asalin garin Ota, ya kama rajistar kotun, Kareem Tolulope.
Wata majiya ta ce wanda ake zargin, a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, ya kutsa cikin ofishin da ke ajiye janareta ta hanyar kwance makullin ginin.
Majiyar ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da ranar hutun da gwamnatin jihar ta ayyana na karbar katin zabe na dindindin domin aikata laifin.
Jami’ar hukumar kula da ma’aikata ta karamar hukumar, Mercy Ajewole, ta kuma tabbatar da cafke wanda ake zargin.
Ta ce Olaniyan ya amsa cewa ya shiga sakatariyar ne ta hanyar tsallake shingen, inda ta ce an mika shi ga ‘yan sanda.
Ta kara da cewa “Abubuwan da aka same shi a kai su ne screwdrivers biyu da jaka guda.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi, bai samu damar jin ta bakinsa ba domin jin ta bakinsa.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga