Daga Shamsu S Abbakar Mairiga.
Jami’in rundunar ƴan sandar jihar Ogun, sunyi nasaran cafke wani ɗan shekara 40 mai suna “Taofeek Sulaiman” wanda ya jima yana lalata da ƴarƴar matar sa yar shekara 13.
Jami’in hulɗa da jama’a, “SP Abimbola Oyeyemi” ya tabbatar da aukuwan lamarin.
Yace “mai laifin an kama sane, bayan korafi da aka kawo a shelkwatar ƴan sandar ta “Owede-Yema” wanda ƙorafin ya fito ne daga mahaifiyar yarinyan. Inda takara da tace, tana yin aure ne da mailaifin, bayan mutuwar mijinta na farko, wanda shi ne babban yarinyan”
Jami’in Yace, “matar ta bayyana cewa, ɗiyar tata tagaya mata ne cewa, mai laifin Ya ɗauki tsawon lokaci yana lalata da ita tun a “14, October, 2022” kana yace zai kashe ta, muddan tagaya ma wani.
Bayan tambayan mai laifin, ya amsa laifin sa. inda yace sharrin sheɗanne.
Daga bisani ƴan sanda suka kai yarinya zuwa ga babban asibiti, domin bata kyakkyawar kulawa.