Yanda wani mutun a Jos ya fille kan matarsa, da datse hannun ‘yarsa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani mutum mai suna Chayi bayan da ake zarginsa da sare kan matar tasa tare da datse hannun ‘yarsa a unguwar Kampala da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.
Lamarin, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, a ranar Talatar da ta gabata ne matar da ta bar mijin ta biyo bayan cin zarafinta a gida, ta je gidan tare da ‘yarta ‘yar shekara shida domin kwashe kayanta.
Wani makwabcin mai suna Sunday Yaks, wanda ya zanta da manema labarai da suka ziyarci al’ummar, ya ce:
“Al’ummar Kampala a halin yanzu suna cikin kaduwa kan abin da mutumin ya yi wa matarsa da ‘yarsa. Na san mutumin da Mista Chayi, kuma sunan ‘yarsa Jessica, ‘yar shekara shida.
“Mutumin yana fama da rikicin aure, kuma matar a ƙarshe ta bar auren tare da ƙaramar ‘yarta.
“Amma matar ta koma gidansu da ke Kampala tare da ‘yarta karama don kwashe kayanta, ba mu san abin da ya faru ba amma sai mutumin ya yanke kan matar da hannun ‘yar da gatari.
“Abin takaici ne yayin da wasu ’yan unguwar da aka sanar da su suka garzaya gidansu. An garzaya da mutanen biyu asibiti, amma matar ta rasu ne a lokacin da take jinya.
“An dauki matakin ne jami’an tsaro suka shiga domin ceto mutumin daga halakar da wasu fusatattun jama’a suka yi masa.”
Kakakin ‘yan sandan, Alfred, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan sandan da aka tura wa al’umma sun kama mutumin bayan samun labarin.
“A yanzu haka, mutumin yana hannun mu. Za a gurfanar da shi gaban kotu idan aka kammala bincike a kan lamarin,” inji shi.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.