Yanda wasu ƴan bindiga su ka kai hari a garin kauyen Gambar, tare da kashe mai anguwa a Bauchi.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da sanyin safiyar ranar Asabar din da ta gabata, sun kai farmaki kauyen Gambar Sabon Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi inda suka kashe mutum biyar ciki har da mai unguwar.
Wani mazaunin unguwar ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun afkawa kauyen ne da manyan muggan makamai inda suka rika harbin iska don tsoratar da mazauna kauyen kafin su aikata laifin da suka aikata.
Maharan sun kuma yi garkuwa da wani Mista Daniel a lokacin harin.
Wani mazaunin yankin, Mista Manasseh Danladi, ya ce: “A jiya (Asabar) wasu mutane sun zo kauyenmu suka kashe kawuna tare da wasu mutane hudu, yayin da aka tafi da Mista Daniel zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba. Har yanzu ba mu kulla alaka da su ba.”
‘Yan sanda sun kashe mutane 12 da ake zargin ‘yan fashi ne, masu garkuwa da mutane a Bauchi
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Lahadi.
Ya ce rundunar ta tura jami’an bincike karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen da ke ofishin ‘yan sanda na Tafawa Balewa domin kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin da ke yankin domin kula da lafiyarsu.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.