Yarinyar Da Mahaifinta Ya Bayarta Cikin Rashin Sani A Bauchi,Tace Tanason Mijin Ta.
Duk da kin karbar sadakin mahaifinta, bayan bayar da aurenta ga wani matashi kyauta a cikin wasa na subul da baki
Yarinyar da aka bayar ta ce tana son mijinta, kuma tana bukatar a gaggauta yi masu biki.
Idan masu bibiyar mu basu manta ba, kwana biyu da suka wuce ne wani abin al’ajabi ya faru a jihar Bauchi inda Wani mahaifi Yayi Subul Da Baki Ya Aurar Da Yarsa Ba Tare Da Ya Sani Ba.
Abun ya faru ne a unguwar wuntin dada dake Bauchin ta yakubu inda magidanci mahaifin wata yarin ya da ake kiranta da Suna nana ya halarci wani daurin aure inda a wajen daurin auren yake gaisawa da wasu samari da yazo kan wani matashi sai yace bazai gaisa da shi ba tunda bashi da mata, a cikin raha.
Shi kwa matashin budar bakin sa sai yace to ai baba kana da yaya mata idan zaka bani Nana zan aureta, nan take mahaifin yarinyar yace na baka ita sadaki daga naira goma zuwa naira dari, nan take cikin abokan matashi wani ya zaro dubu hamsin ya bayar wani ya bada dubu goma har kudi dai yakai kusan dubu dari .
Amma daga bisani mahaifin yaki karbar sadakin yace da wasa yake,
Sai dai kuma a bangare guda Malam Mustafa baba ilaila fitaccen malamin addinin musulunci ne a jihar Bauchi kuma shugaban hukumar shari’ar musulunci ne a jihar yace aure ya riga da ya dauru tunda uba shi yace ya bada ita, kuma har an hada sadaki illa iyaka bai karba ba ne dan haka aure ya dauru
Sannan shima babban malamin addinin musulunci Shaikh Idris Abdulaziz ya kawo hadisi wanda yake nuna cewa aure dai ya dauru yanzu abu daya kawai ya rage shi ne a sanarwa da yarinya.
Cikin yardar Allah bayan da yarinya ta samu labarin tace tanason mijin ta
Shin wace shawara zaku ba wa mahifinta da ke ci gaba da turjiyar kin karbar sadaki?