Wani yaro dan shekara 10 ya kashe mahaifiyanshi saboda taki saya masa na’uran wasa a Amurka.
Bayan yaron ya bindige mahaifiyan shi, yaci gaba da shiga cikin asusunta na amazon washe gari kuma ya sayama kanshi na’uran kai ta Oculus Virtual Reality.
A cewan jaridan NEW YORK, an tuhumi yaron da laifin kisan kai na farko kuma yana tsare a wani wurin tsare yara kanana.
‘Yar uwanshi mai shekaru 26 ta kai kara wajen ‘yan sanda, inda yaron ya shaidawa ‘yan sandan cewa ya nunawa mahaifiyan shi bindiga yana mai gargadin ta akan zata saya mishi na’uran ne koya harbeta, sai uwar taki ta amsa yaron yasaita kuwa ya harbeta a fuska.
An tuhumi yaron mai shekaru 10 a matsayin babban mai lefin kisan kai na matakin farko zai bayyana a cibiyan da ke Milwaukee a ranan 7 ga Disamba.
Wakiliyan shari’a ta yaron Angela Cunningham, tace haryanxu tana tattara bayanai game da lamarin.
Wannan babban bala’i ne na iyali banajin wani zai musanta ko rashin yarda da hakan inji Mista Cuningham.
Rahoto: Hajiya Mariya Azare.