Yunkurin Sabbin Rushe-rushe A Kaduna: An Maka El-Rufai A Kotu.
Daga Muhammad A. Dalhatu
Sabon yunkurin da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ke yi na ci gaba da rushe-rushen gine-gine a jihar ya haifar da cece-kuce da sabbin kararraki a kotunan jihar, inda aka nemi kotu da ta dakatar da shi bisa wannan aiki na rashin bin ka’ida.
A wata takardar kara da aka shigar a gaban babbar kotun Kaduna mai dauke da lamba KDH/KAD/515/23; makarantun Imam Sadiq Academy LTD, Tahfiz Fudiyyah Zaria, Fudiyyah Nursery and Primary Schs., Saminu Kusa Muhammed, Ahmad Abubakar, Haruna Danfulani U/Mu’azu, Shuhada Foundation, a madadinsu da kuma ‘Yan Shi’a mazauna jihar Kaduna sun maka gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Gwamnatin jihar Kaduna, Ma’aikatar Gidaje da ci gaban Birane ta jihar Kaduna, KASUPDA, da kuma Daraktan KASUPDA, Isma’il Umaru Dikko a gaban kotun ne bisa yunkurin da suke yi na rusa musu muhallai ba bisa ka’ida ba da kuma sunan cewa na ‘IMN’ ne.
Masu shigar da karar sun ce wadannan muhallai ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da abin da wadanda aka maka gaban kotun suke ikirari. Inda suka nemi kotun da ta dakatar da su.
Karar wanda aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kaduna, har wala yau kara neman da kotun ta bayar da umurnin hana rushe musu muhallai da sunan cewa na ‘IMN’ ne. Inda suka ce gine-ginensu ne da suka gina bisa ka’idar doka, kuma suna da dukkanin wani shaida na yin gini a jihar ta Kaduna.
Sannan sun kuma nemi kotun da ta ci tarar wadanda ake kara inda aka same su da wannan laifi bisa wannan yunkuri da suka yin a rusa musu muhallai.
Wakilinmu ya shaidi shaidar shigar da karar wacce aka gabatar a gaban babbar kotun na Kaduna dauke da kwanan wata 18 ga watan Mayun 2023.
Idan ba ku manta ba, kafafen watsa labaran Nijeriya sun labarto cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da rushe muhallan wadanda ya kira da ‘IMN’ da kuma wasu gine-gine dake Gbagyi da wadansu wurare duk a jihar ta Kaduna kasa da mako 2 ya kammala mulkinsa a jihar ta Kaduna.
El-Rufai ya amince da rushe wadannan muhallai ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 20 ga Afrilun 2023. Inda hukumar KASUPDA ke neman N29,253,500 domin gudanar da aikin.
Cikin adadin wannan kudin, hukumar ta KASUPDA na da bukatar N20,253,500 domin rushe muhallan da ya kira na ‘IMN’.