Yadda Rahotonni suka bayyana cewa, za’a siyar da fitacciyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa na ingila ta “Manchester United” nan ba da jimawa, ba bayan shekaru 17 a ƙarƙashin mallakar Ƴan kasuwar Amurkan wato Glazers, bisani sanarwa ta tabbatar da shirin su na siyar da kungiyar. We
“Avram”, ”Joel”, “Glaze” sunce za su tantance duk zaɓuɓɓuka don tabbatar da cewa sun fi yiwa magoya bayan su hidima da kuma cewa “Manchester United” ta ƙara yawan damar cigaban da ake samu ga ƙungiyar a yau da kuma nan gaba”.
“Majiyoyin sun ba da tabbacin shirin Glazer shine zai siyar da ƙungiyar ɗin nan ba da jimawa ba kuma tsarin yana cigaba da gudana.”
“A halin yanzu dai tuni anfara hada-hafar zaman tattaunawa domin cigaba da tattaunawa na ganin an tabbatar wannan cinikin ƙungiyar ƙwallon ƙafan an kammala da waɗanda suke buƙata.”
“A halin yanzu dai manyan Ƴan kasuwa na duniya ne suka fara zawarcin Neman da’a sayar masu da ƙungiyar ƙwallon ƙafan, inda har yanzu masu ruwa da tsaki na ƙungiyar ƙwallon ƙafan ba su iya tantance wanda za su sayarwa da ƙungiyar ba”
“Idan baku mantaba wasu Rahotonni sun tabbatar cewa, tauraron ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, wato “Cristiano Ronaldo” zai bar ƙungiyar ta “Manchester United” bisa yarjejeniyar a tsakanin sa da ƙungiyar.
“Ƙungiyar ta gode masa saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a tsawon lokuta biyu Na Kakar Wasanni ”2021”, da “2022”
Ɗan Wasan “Cristiano Ronaldo” Ya bayyanan cewa, Bayan tattaunawa da “Manchester United”, sun amince da mu kawo ƙarshen kwantiragin mu da gaggawa.”
“Ronaldo” Yace yana son “Manchester United” kuma yana son magoya bayanta, hakan ba zai taɓa canzawa ba a garesa cikin Tarihi rayuwarsa.”
“Ya ƙara da cewa Koyaya yana jin kamar lokacin da ya dace da shi ne don neman sabon ƙalubale acikin aikinsa.”
“Ronaldo” Ya Kuma Bayyana cewa, yana yiwa “Manchester United” fatan samun nasara a sauran kakar wasanni da kuma nan gaba.”
Labari: Bashir Muhammad Maiwada.