Za’a rika tuna Mijina Musamman kan halaccin da yaiwa Matasa – A’isha Buhari.
Aisha Buhari ta bayyana cewa mijinta Shugaba Muhammadu Buhari, ya bai wa hidimar matasan ƙasar nan muhimmanci sosai.
Ta bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wani shirin kiwon lafiya da matasa masu yi wa kasa hidima suka kaddamar a Abuja.
Ta bukaci matasan su ci-gaba da yin aiki tukuru wajen ganin an ci-gaba da samun wanzuwar hadin kai a kasar nan.
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta ce za a rika tuna mijinta Shugaba Buhari a matsayin shugaban kasan da ya baiwa matasa muhimmanci.
Ta bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wani shirin tallafin lafiya ga mutanen karkara (HIRD), na hukumar matasa masu yi wa ƙasa hidima, NYSC, a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ta kara da cewa shugaba Buhari mutum ne da ke matukar son shirin na masu yi wa kasa hidima wato NYSC, saboda yadda ya ke son ganin hadin kan ‘yan Najeriya.
Ta kara da cewar saboda da kaunarsu da Buhari ya ke yi, sukan gayyaci matasan masu yi wa ƙasa hidima zuwa gidansu da ke Daura a duk lokacin bukukuwan sallah.
Aisha Buhari ta yi kira ga masu gudanar da shirin da kada su yi kasa a gwuiwa wajen tabbatuwar hadin kan ‘yan kasa ta hanyar hidimtawa al’umma ba tare da la’akari da jiha ko wurin aiki ba.
Ta kuma ce shirin na HIRD ya kayatar da ita sosai, a dalilin haka ne ma ofishinta ya bayar da gudummawar kayan aikin asibitin tafi da gidanka don habbaka nasarar shirin.
Ta kara da cewa shirin ya yi matukar tasiri musamman ma a yankuna na karkara, wanda a dalilin hakan ne shirin ke ci-gaba da samun yabo daga ciki da wajen kasar nan.
A bangaren, Darakta Janar na hukumar masu yi wa kasa hidima, NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ya ce an kirkiro shirin na HIRD ne a 2014 saboda taimakawa marasa karfi da ke a yankunan karkara.
Ya ce shirin ya kunshi ‘yan bautar kasa da suka hada da likitoci, masu bada magunguna, ma’aikatan jinya, likitocin hakori da sauransu, wadanda suke duba marasa lafiya a kyauta.
The Guardian ta ruwaito Ahmed ya na fadin cewa kawo yanzu sama da ‘yan Najeriya miliyan uku ne suka ci gajiyar shirin.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.