Zamu Rika Biyan Masu Tu’amali da Twitter Duk Wata Cewar Elon Musk Mai Kamfanin Twitter
Elon Musk, mai kamfanin Twitter, ya yi alkawarin fara biyan masu kirkire cikin makwanni masu zuwa yayin da yake ci gaba da yin sauye-sauye a kamfanin
Musk ya kuma bayyana cewa zubin farko na biyan zai kai kusan dala miliyan 5, kuma komai a shirye yake
Sai dai, ba kowa ba ne zai amfana daga tsarin, saboda ya kafa sharudda ga masu sha’awar samun kudi a Twitter
Twitter, fitacciyar kafar sada zumunta, na shirin gabatar da wani sabon shirin da zai bai wa jama’ar da ke da dangwalen ‘verification’ damar samun kudi a kafar.
Elon Musk, mamallakin kamfanin da ya saye shi a watan Oktoban bara ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cewarsa, ana sa ran zubin farko na kudin da zai biya zai kai kusan dala miliyan 5 wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.3.
Sai dai, Musk ya jaddada cewa masu tabbataccen asusu ne kadai za su ci gajiyar wannan shiri, kamar yadda rahotannin CNN suka bayyana.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Twitter ke fuskantar kalubale wajen rike masu ba shi talla bayan da ya yi koran ma’aikata da yawa.
Sayen da Elon Musk ya yiwa Twitter ya jawo raguwar amintar masu daura talla, yayin da suke shakkar sanya tallansu akan dandamalin.
Bugu da kari, kaddamar da cajin $8 kowane wata ga masu asusun da ke da dangwalen ‘verified’ ya gamu da turjiya da suka daga fitattun ‘yan soshiyal midiya.
Musk ya yi cikakkun bayanai game da shirin biyan kudin yana mai bayyana cewa za a fara biyan masu asusun da ke da ‘verification’ nan da ‘yan makwanni kuma ya bayyana cewa za a biya su kudi ne kan tallan da aka nuna a kan shafukansu.
Wannan ne dai karon farko da Twitter zai fara irin wannan lamari, yayin da kamfanonin sada zumunta irinsu Facebook suka jima da fara biyan masu talla.
An yi ta cece-kuce a kafar Twitter lokacin da Musk ya bayyana fara karbar kudi kan duk wani asusun da ke neman ‘verification’.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim