Zan bawa Ma’aikatan Jihar Kaduna fifiko da jin dadinsu, zababben gwamna Uba Sani.
Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba sani a Sakon sa na ranar ma’aikata Yana cewa Ina taya ma’aikatan Najeriya da kungiyar kwadago murnar zagayowar ranar ma’aikata na watan Mayu. Kun bayar da gudunmawar da ba za ta iya misaltuwa ba wajen gina kasa da wadata kasar Najeriya. Abubuwan sadaukarwar ku suna na rubuce kuma ƴan Najeriya suna mutunta hakan sosai.
Al’ummarmu ta sha fama da kalubale. Abin farin ciki ne a lura da cewa ba ku yi kasa a gwiwa ba a kan imanin ku ga kasa da kuma sadaukar da kai ga ci gaban kasa da ci gaban wadata da zaman lafiya Kun kare dimokuradiyyar mu da yancin jama’ar Najeriya. Kuna tsayawa kan hadin kan kasa a kowane lokaci. Ma’aikatan Najeriya da kuma ’yan kwadago su ne ginshikan ci gaban Najeriya da hadin kan kasa.
A wannan karon da ba a mantawa da shi ba, ina mika godiya ta musamman ga ma’aikatan jihar Kaduna masu jajircewa da basira da kwazo. Kun jajirce da kwazo wajen ganin ci gaba da cigaban wannan jiha tamu. Gwamnatina za ta kasance abokiyar aikin ku. Zan ba da fifiko ga jin daɗin ku kuma in samar muku da kayan aiki da abubuwan ƙarfafawa waɗanda za su taimaka haɓaka himmar ku don yin aiki mai kyau. Za a ba da lada ga aiki tuƙuru. Duk abin da nake nema shi ne haɗin kai da sadaukarwar ku gaba ɗaya.
Barkanku da ranar ma’aikata.