“Zan kai bankuna ƙara kotu, saboda sun sa nabar iyalina cikin yunwa” wani dattijo ya koka.
“Zan kai su kotu, saboda iyalina suna jin yunwa, ina ganin ya kamata mu je kotu”
Wani dattijo dan Najeriya ya fusata sosai bayan ya ziyarci banki domin cire kudi daga asusunsa
A cikin wani faifan bidiyo da ke tafe, ya ga jerin gwano a bankin suna tururuwa don karbar kudi da kansu.
Mutumin cike da bakin ciki ya koka kan yadda ya kasa cire kudi daga asusun sa, duk da ya dade a wurin.
Ya koka da yadda matansa da ’ya’yansa ke fama da yunwa a gida, ya kuma yi barazanar kai bankin kotu domin su karbi kudadensu.
A cikin maganarsa “ni ba maroƙi ba ne. muna zuwa ne don kudin da muka sanya a nan. don haka abu na gaba shi ne kotu ta tilasta musu su ba mu kudinmu. muna jin yunwa a gida. ba za mu iya ci a gida ba. ‘ya’yanmu suna jin yunwa. matan mu suna jin yunwa.
“Na zagaya kasashen Turai kuma ban taba ganin irin wannan a duniya ba”
“Banki ba su ma damu da mu ba. ina ganin ya kamata mu je kotu. Ba zan iya yin komai ba. Domin sun kulle min kofa. babu wanda zai iya bayyana mani abin da ke faruwa.”
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.