Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin mayar da matatun man kasar guda uku zuwa wani kamfani domin tara dala biliyan 10 domin karfafa kananan ‘yan kasuwa da masu karamin karfi a kasar nan.
Atiku, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wani gangamin yakin neman zabe jiya a Legas, ya bayyana matatun man da na Warri da Fatakwal da kuma Kaduna.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce zai bi tsari mai wajen sayar da kamfanonin, idan aka zabe shi Shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Ya ce: “A nawa bangaren, idan ka zabe ni a matsayin shugaban kasa na ce kuma na yi alkawari da yardar Allah zan ware dala biliyan 10 domin mu karfafa wa matasanmu maza da mata kanana da matsakaitan kamfanoni.
“Mutane suna tambayana inda zan samu kudin, idan na sayar da matatar mai ta Fatakwal, da matatar mai ta Warri, da matatar mai ta Kaduna, zan samu kudin.”
Dan takarar na PDP ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin kasar, idan aka zabe shi Shugaban kasa a 2023.
“Don haka ni ma ina yi muku alkawari, idan kuka zabe ni za mu sake fasalin kasar nan, me muke nufi da sake fasalin kasa, za mu ba jihohi da kananan hukumomi karin iko da albarkatun kasa, ya rage gare ku ku dora musu alhakinsu. .”
Har ila yau, fitattun jiga-jigan jam’iyyar PDP ba su halarci taron gangamin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a dandalin Tafawa Balewa da ke Legas, a jiya.
Shugabannin sun hada da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (Kudu) Cif Olabode George.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.