Zanga-zangan Neman Sakin Emefile Na Dab Da Barkewa A Nijeriya.
Daga Al-asad Al-Amin Funtua.
DSS Ta Gargadi Kungiyoyin Da Ke Shirin Gudanar Da Zanga-Zanga A Legas Da Abuja Domin Neman A Saki Emefiele.
Rundunar ‘yan sandan sirrin Najeriya DSS ta bakin mai magana da yawunta, Dr Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce kungiyoyi suna niyyar shirya zanga-zanga a wurare daban-daban a Abuja da Legas dauke da allunan kira da a gaggauta sakin gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele.
A ranar Asabar ne hukumar ta yi gargadi ga mutane da kungiyoyi wadanda ta ce ta gano cewa suna shirin gudanar da zanga-zanga ga gwamnatin tarayya kan dakatarwar da kuma tsare Mista Godwin Emefiele.
Afunanya ya ce, “Kungiyoyin sun yi niyyar haduwa ne a wurare daban-daban a Abuja da Legas dauke da allunan da ke nuna Hukumar da Gwamnatin Tarayya da yin kira da a gaggauta sakin Emefiele.
Don haka hukumar ta gargadi wadanda ke da hannu wajen shirya zanga-zanga da su daina. A halin da ake ciki hukumar ta ce ta baiwa iyalan Emefiele da jami’an kiwon lafiya da kuma wadanda suka dace damar ganawa da shi tun daga ranar da aka kai shi, bayan samun umarnin kotu na yin hakan.
A farkon makon nan ne dai Emefiele ya bayyana tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa, a matsayin wanda ke da hannu a badakalar sake fasalin kudin Naira da ta addabi kasar watannin baya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ta ALFIJIR HAUSA ta samu labarin cewa Emefiele wanda jami’an ‘yan sandan sirri na kasar ke tsare da shi ne ya sa aka gayyato shugaban hukumar ta EFCC wanda hakan ya yi sanadiyar tsare shi.
A daren Larabar da ta gabata ne hukumar DSS ta gayyaci Bawa hedikwatar ta da misalin karfe 9:02 na dare. Daga nan sai jami’an ‘yan sandan sirri suka tsare shi. Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi.
Gayyatar Bawa da DSS ta yi ya zo ne kwanaki bayan da aka kama Emefiele aka dauke shi daga Legas zuwa Abuja don fuskantar tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa da wasu tuhume-tuhume.
Emefiele da Bawa – wadanda ke fuskantar tuhume-tuhume – ana yi musu tambayoyi ne kan batutuwa daban-daban da suka hada da badakalar sake fasalin Naira.
A ranar 23 ga Nuwamba, 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari na lokacin tare da Emefiele sun kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira 200, Naira 500 da Naira 1,000. Emefiele ya nace cewa tsoffin takardun za su daina amfani daga ranar 31 ga Janairu, 2023.
Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Emefiele ya dage kan cewa wannan matakin ba wai a kan kowa bane domin akwai rade-radin cewa wasu ne daga fadar shugaban kasa ne suke yunkurin hana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC) mai mulki a wancan lokaci samun nasara a zaben Fabrairu 25, 2023.
Tsarin sauya fasalin kudi dai ta janyo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba a taba ganin irinsa ba, sakamakon karancin kudin da ake samu na Naira, inda CBN ta kasa samar da sabbin takardun kudi
Tsarin ita ce ta haifar da matsalar kudi da kuma dogayen layi a bankuna da na’urar cirar kudi ta ATM. Tinubu ya dakatar da Bawa daga ofishinsa a ranar Laraba, yana mai cewa hakan zai ba da damar gudanar da cikakken bincike a kansa da ya ke ciki a lokacin da yake kan mukaminsa a baya, sakamakon “manyan zarge-zarge” na amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba.