Zanyi kewar Mutanen kirkin da nayi aiki tare da su tsawon shekaru takwas, Buhari.
Babban Abin Da zan yi Kewa Bayan Na Sauka A Mulki Shugaba Buhari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin abinda zai yi kewa idan ya bar kan madafun ikon kasar nan.
Shugaba Buhari ya ce zai yi kewar mutanen kirkin da ya yi aiki tare da su na tsawon shekara takwas a gwamnatinsa
Shugaban kasar na ta shirye-shiryen yin bankwana da madafun ikon ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana babban abinda zai yi kewa sosai bayan ya mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, shugaba Buhari ya ce bayan ya bar mulki zai yi kewar mutanen da ya yi aiki tare da su a gwamnatinsa, wadanda ya kira da mutanen kirki.
“A birnin Landan sati biyu da suka gabata, da ni da sauran yan jaridar fadar gwamnati, mun tambayi shugaban kasa abinda zai yi kewa sosai idan ya sauka daga mulki.”
“Ya ba mu amsa da cewa zai yi kewar mutanen kirkin da ya yi aiki tare da su a shekara takwas da suka gabata, kamar wasu daga cikin mu da ke a wajen.”
Da ya ke magana kan aikin da ya yi, Adesina ya ce ya hidimtawa shugaban kasar iyakar iyawarsa, sannan zai bar Villa a matsayin wanda ya samu cikakkiyar gamsuwa na sauke nauyin da aka ɗora masa, cewar rahoton PM News.
“Aiki na ya kare, na tattara yan jakunkuna na sannan na shirya barin Villa. Lokacin da zan fice daga fadar shugaban kasa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayun 2023, shine zai zama na karshe a matsayin dan cikin gida. Idan har na kara dawowa, sai dai a matsayin bako wanda ya kawo ziyara.” A cewarsa.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.