Zanyi sadaka da kafitanin dukiyana na umarci ɗa na da ya je ya nema nashi – Jackie Chan.
Shahararren dan wasan fim din turanci da na china, Jackie Chan ya bayyana cewa yana shirin yin sadaka da dalar Amurka miliyan 400 wanda ya samu ikon tarawa sama da shekaru 60 a matsayin dan fim, kuma ba zai bar wa dansa ko kobo ba.
Jackie yana son Jaycee ya zama ya samu kudi da kansa, Don haka, ɗan wasan ya yanke shawarar yin kyauta da miliyoyin kudadensa maimakon bar wa ɗansa gado.
Chan yace: “idan ya dauki aikinsa da sana’arsa da muhimmanci, zai iya samun kudin kansa, idan kuma ba haka ba, to sai ya rika bata nawa.”