Zargin Mijinta Dauke Da Kaurin Ruwan Kwayan Halitta Mata Ta Nema Saki.
Wata Amarya Ta Kai Ango Ƙara Kotu, Ta Nemi a Raba Auren Saboda Yana da Matsalar Kaurin Ruwan Kwayar Halitta.
Wata matar aure mai suna Salamat Suleiman ta maka mijinta a kotu wata biyu bayan sun yi saboda wai maniyyin mijinta bashi kauri.
Salamat ta bayyana a kotun Ilori, jihar Kwara cewa ta gaji da wannan aure ba za ta iya ci gaba da shi ba.
Amma kuma mijin Salamatu bai karyata hakan ba sai dai ya shaida wa kotu cewa ba shi da cikakken lafiya ne ya sa maniyyin sa sai ya fito kamar ruwa ba kauri, amma yana son matar sa.
Ya ce ita ma Salamatu ba isasshen lafiya ta ke da shi ba. Mijin ya roki kotun da ta bashi damar sassantawa da matarsa.
Alkalin kotun AbdulQadir Umar ya shawarci Salamatu da kada ta kashe auren ta saboda ko wani aure da nashi matsalar.
Sannan kuma ya umarci Salamatu da mijinta su garzaya asibiti dukkan a duba su a basu magani don su warke.
Ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 28 ga Agusta
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.