Malam Nata’ala Mohammed, mai taimakawa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Sen. Abdullahi Adamu, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa akan cewa faifan bidiyon wani mutumi da ya tuɓe tsirara a fadar sarkin Lafia ana zargin Adamu ne.
A wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho ranar Asabar a Keffi, Mohammed ya ce waɗanda ke yin irin waɗannan zarge-zargen ba su da tabbacin gaskiya ga kansu, ya kuma ƙara da cewa, “suna neman dacewa ne kawai kan ganin su tozarta.”
” Wani hoton bidiyo na wani mutum da aka tuɓe tsirara a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba a fadar Sarkin Lafiya, wanda kuma aka yi ta yaɗawa da kuma zargin cewa shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa to ƙarya ne.
” Hasashen miyagu ne kawai waɗanda ba su san kamannin Sen. Abdullahi Adamu ba.
Mohammed ya ce: “Wannan mummunan halin rashin muhalli na zahiri ne, ba za a danganta shi da shi ba,” in ji Mohammed.
Har ila yau, wata ƙungiya mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, A .A Sule Progressives Forum, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan mugunyar aikin da ya faru ga Babban ubangidansu, Alhaji Abubakar Giza, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Ciroman Giza.
Ko’odinetan taron na Jiha, Mista Jonathan Samuel ya bayyana faruwar lamarin a matsayin na dabbanci kuma bai dace ba.
Ya bayyana cewa Giza dattijo ne kuma jigo a jam’iyyar APC wanda ya kasance ginshikin goyon bayan gwamnatin jihar Nasarawa.
A cewar Samuel, Giza mutum ne mai son zaman lafiya, yana mai cewa, “kada a yi watsi da mugun aikin da wasu marasa gaskiya suka yi masa.
“Ya kamata a gano waɗanda suka aikata irin wannan aika aika a gurfanar da su gaban kuliya domin yazama izna gawasu.”
Ya jaddada buƙatar kowa da kowa su kasance masu lura da tsaro a kowane lokaci, yana mai cewa, “waɗannan miyagun marasa kyau suna ɓoye a ko’ina.”
Samuel ya kuma Buƙaci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen cafke masu irin wannan laifin.
RAHOTO:- Comrd Yusha’u Garba Shanga