Zawarawa sun yi bikin Mutuwar auren wasu Mata tare da yi masu rijista a ƙungiyarsu.
Zawarawa Na Bikin kaddamar da sabbin zaurawa Da Su Ka Shiga Kungiyar Ta Su Na Zaurawa.
Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta ya jawo martani daga mutane da dama bayan an gano kungiyar zaurawa na biki
A faifan bidiyon an gano kungiyar zaurawan na bikin karbar sabbin mambobinta a Port Harcourt babban birnin jihar Rivers
Wanda ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na Twitter ya bayyana yadda suke gudanar da bikin nasu na karbar sabbin mamabobin
A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, an gano kungiyar zaurawa suna bikin karbar sabbin mambobi don shiga kungiyar.
Wanda ya wallafa faifan bidiyon Abdullah Ayofele a shafinsa na Twitter ya ce bikin ya gudana ne a Port Harcourtbabban birnin jihar Rivers.
Ya yin da Ayofele ya yi rubutu a saman faifan bidiyon kamar haka (Wahala Wahala Wahala).
“Taron kungiyar zaurawa na bikin karbar sabbin mambobi yayin da suka yi wa bikin lakabi da ‘Karshen matsala’ ka yi rayuwa ba takurawa a Port Harcourt, taken kungiyar shine “Nayi, Na kara yi, kuma na gama…….hahah.”
Sannan akwai kek mai dauke da “Nayi, na kara yi kuma na gama” wanda daya daga cikin matan ta dauka yayin da sauran mata suke cikin nishadi.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan faifan bidyon.
@arcadol:
“Abin da ubangiji ya hada wa ya isa ya raba? Bai kamata mu rinka kula da wadanda muke tare da su ba? #Aljanu.”
@gbonjunbolaO:
“Me yasa maza suke kuka duk lokacin da mata suka nemi saki? Rabuwan yafi konawa maza rai fiye da matan.”
@GentleTLADY:
“Kayi tunanin in ‘ya’yansu suna wurin za su ce su ma wataran matansu ne anan sun hadu da iyayensu, za su kasance su kuma kaman iyayensu maza,”
@Dami4Change:
“Farin ciki kyauta ne.”
@AdebowaleShogb3:
“Tun da a Port Harcourt ne manta mallam. Wadanda kuke gani anan kadanne, da yawansu suna gidajen mazajensu amma ba zaman aure ba.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim