Da fitowarsa ba tare da tuna ko shi wanene ba muka fara hira kamar mun dade da sanin juna, har na ji na sake… Iyalansa suka fito matarsa da yaransu hirar Ilmi ta barke kamar ina cikin ‘yan uwana, Lallai a nan na fahimci ma’anar Kalmar Yan uwa ko Ikhwaan ko Brothers da ake kiran jamaarsa, duk abinda suke akwai wannan yan uwantakar a ciki.
Falonsa duk inda na daga kai zan hada ido da hoton wani daga cikin shahidan iyalansa, wanda hakan ke nuna cewa ana cikin kewa da damuwa da wanda aka rasa, jinjina gwarzantakarsa da jinjina zalumcin da aka masa, amma kuma hakan bai hana dariya da walwala irin ta me bar wa Allah lamari ba.
Shehun na son yayi min kyautar litattafai amma duk sunan Littafin da ya kama idan aka je dubawa sai a samu tuni jami’an tsaro suka salwantar da su ko dai ta yawan sumamen da suka sha kai masa ko kuma yadda ake rusa masa mahalli a ta da shi daga matsuguninsa, a wannan lokacin babu abinda nake tunawa sai magana Dan kare hakkin dan Adam din nan na zamanin Firauna, wanda Allah ya sakaye sunansa da Rajulun min Aali Fir’auna, Inda yake cewa( Wai zaku kashe mutum ne kawai don ya ce Allah ne ubangijinsa?) Suratu Yasin..
A yayinda yake lissafo laifukan da aka tuhuma shi da su kada bakin matarsa Malama Zinatu sai tace “Ni kuma da aka daure shekara 5 ba tare da wata tuhuma ba, ko dai laifin shine matarsa ce oho” na juya da sauri na kalli baiwar Allahr nan, An yi mata lahani har yanzu jikinta da akwai albarusai, bata da lafiyar kafa, amma wai har a kotu ba a iya kawo laifin da ta yi wa jami’an tsaro da aka daure ta na shekara biyar ba, kuma ba a biya ta diyya ba!!!
Amma kun san wani abin sha’awa? Duk wannan hira da ake cikin farinciki da walwala da fara’a ake yi, Mutumin da ya shirya bayar da Ransa ga imaninsa ba shi da wata damuwa, hana rantsuwa na kan ga bacin rai ya bayyana ne a fuskar malamin idan ya tuno wata hasara ko tuggu da ake shirya wa Musulunci ko kuma yayin bani labarin wani abu da aka yi ba tare da neman yardar Allah ba.
Sannan mafi yawan zaman kamar yadda za ku gani a hoto an yi shi ne cikin sha da shayarwar Ilmi, Malamin ya shayar da ni ilmi akan Tarihi, Ibada, ‘yancin mata, muhimmancin hadin kan musulmi,da kuma makircin da ake shirya wa Musulmi wanda babu me musa cewa ko an ki Allah an san cewa akasarin hasashensa ya bayyana gare mu a gaske, inda dole mu yarda cewa Ko dai me tarin Ilmi ne na gidi ko kuma yana da wata Ilhama da yake sha daga Wa’atainahu Min ladunna Ilma.
ZIYARAR SHEKH ZAKZAKY Ita ce ziyara mafi dadi da amfani da na yi a wannan shekarar zuwa yanzu, kuma ko yanzu na sami karin wannan ziyara ina kwadayinta. Hakika ziyarar wanda aka cuta ta fi ziyarar macuci dadi.
Daga Rahma Abdulamjib