Gwamna Zulum ya sha Alwashin Hana ƴan adawa samun nasarar komai a Borno.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da kwamitin da za suyi wa APC aikin kamfe a Borno
Gwamnan ya bukaci ‘yan kwamitin su dage wajen ganin jam’iyyar APC ta doke kowa a zaben 2023
Zulum ya bada hakuri ga Atiku Abubakar a kan harin wasu bata-gari suka kai wa tawagarsa kwanaki.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya sha alwashin ganin jam’iyyar APC ta lashe duk wani zabe da za a shirya a shekarar 2023.
Babagana Umara Zulum yana so a hana jam’iyyun adawa lashe ko da a rumfa daya ne a fadin jihar Borno a mulkinsa,Vanguard ce ta fitar da rahoton nan.
Mai girma Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya hadu da magoya baya da masu ruwa da tsaki wajen kaddamar da kwamitin yakin zaben APC.
Jam’iyyar APC ta reshen jihar Borno, ta rantsar da mutum 800 da za suyi mata yakin zabe. An kaddamar da ‘yan kwamitin a gidan gwamnati na Maiduguri.
An rahoto Gwamnan yana cewa abin dariya ne an samu wasu sun lallabo a karkashin jam’iyyar PDP da ta mutu, suna neman mutane su zabe su.
Farfesa Babagana Zulum ya zargi ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da jawo rigima da sunan yin kamfe. An ji shi a shafinsayana cewa ya cika alkawarin da yayi a 2019.
The Nation tace Gwamnan ya yi amfani da damar wajen bada hakuri ga Atiku Abubakar, a dalilin harin da tsageru suka kai wa tawagarsa wajen kamfe.
A jawabin da ya gabatar a jiya, Farfesa Babagana Zulum ya tunawa ‘yan adawa cewa Borno jihar APC ce, la’akari da irin abubuwan da ya yi a cikin shekaru uku.
Duk da haka, Farfesan yace jam’iyyar APC ba ta tsoron wata jam’iyyar adawa da ke neman zabe.
Zulum yana tunkaho da cewa gwamnatinsa ta bunkasa harkar tsaro, ta kawo ayyukan yi, ta tallafawa matasa, kuma an maida mutane garuruwansu.
Shugaban APC na Borno, Alhaji Ali Dalori ya yabi Gwamnan amma ya nuna bai ji dadin rashin halartar Hon. Muktari Aliyu Betara wajen rantsarwar ba.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.