Daga Muhammad Inuwa Zariya.
Macijiyan da tayi rayuwa da sarauniya Amina, macijiyan me kimananin shekaru 963 a duniya tayima mazauna wajan gargaɗi, gargadin dai yafarune ta yadda ta tayar da hankalinsu da kuka da fitar da wani hayaki daga kogonta dake kan dutsen turunku.
Mazauna wajan dai sun zargi hakan ya faru ne sabo da wani maciji da aka kashe bayan ya sakko daga dutsan zuwa kasa inda mutane ke gudanar da al-amuransu.
Bugu da ƙari macijiyar ta nema data fara ɓarna kan abubuwa da dama haka musamman na hana al’umamr Turunku dake Karamar Hukumar Igabi Jihar Kaduna zuwa gonakin su saboda da nuna fushin ta kan haka.
Amma tuni al’ummar yankin suka dukufa da addu’oi domin shawo kan Lamarin duba da yadda maciyar ta fusa ta kwarai.