Ku Kawo Kudadenku: Jerin Bankunan Da Suka Kara Ranakun Aiki Don Sauyin Fasalin Naira.
Wasu bankunan Nijeriya sun sanar da sauye-sauyen na lokutan aikinsu don karɓan kuɗaɗen Ƴan Najeriya kafin wa’adin gwamnati ya shuɗe.
Bankuna da sun aikawa kwastamominsu saƙonni sanar da su cewa za’a fara buɗe bankuna a ranar Asabar.
A ranar 15 ga watan Disamba, babban bankin Najeriya CBN ta ce za’a saki sabbin kuɗaɗen N200, N500, N1000.
Biyayya ga umurnin babban bankin Najeriya CBN na tattara kuɗaɗen Naira dake yawo cikin jama’a, bankuna sun fara sauya lokutan aikin su don mutane su samu damar kai kuɗaɗensu.
A saƙon akwatin email da suka aikawa kwastamominsu, bankunan sun bayyana cewa sun sauya ranakun aikinsu ne don taimkawa kwastomomi wajen zuba kudadensu a banki kan ranar 31 ga Junairu da CBN ya bada wa’adi.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa akalla N2.73 Trillion na kudaden Naira dake yawo cikin jama’a zasu dawo banki idan aka sauya fasalin N200, N500, da N1000.
“Zamu tsawaita lokutan aikinmu na mako, sannan kuma zamu fara bude ranar Asabar daga karfe 10 am zuwa 2pm don karban kudade.”
“Yanzu zaku iya kawo tsaffin kudadenku kafin ranar 31 ga Junairu, 2022 da akayi wa’adi. Zamu bude karfe 10 zuwa karfe 3.”
Bankin “United Bank for Africa” (UBA) shima ya ce za’a fara buɗewa ranar Asabar, rahoton “TheCable.”
“Sakamakon sanarwar CBN na sauya fasalin Naira, zamu zamu fara budewa ranar Asabar daga karfe 10:00 na safe zuwa 2:00 don karban kudade kadai.”
Saura bankuna ma sun aika ire-iren wadannan sakonni ga kwastamominsu.
Majalisar dattijai a ranar Laraba ta bayyana amincewarta ga shirinbabban Najeriya (CBN) na sake fasalin kudin Najeriya, The Nation ta ruwaito
Amma ta yi tsokaci da cewa, karshen watan Janairu ya yi kusa ga mayar da kudaden da ke yawo a kasar zuwa banki.
Shugaban kwamiti harkokin banki, inshora da hada-hadar kudi, Sanata Sani Uba ne ya bayyana haka.
Daga Zuhair Ali Ibrahim.
Agaskiya Baba Buhari munyaba sosai da gobnatinka harkar noma da kiyo ta bunkasa a Nigerian naku by Hassan Lawan maigari Wanda akafi saani da Hassan jibiya