SU WAYE HAUSA BAKWAI DA BANZA BAKWAI?
A tarihin da yagabata na Bayajidda ya nuna cewa, Matan da Bayajiddan ya aura wato Sarauniya Daurama da kuma Gimbiya ƴar Sarkin Borno da kuma Baiwa da Sarauniya Daurama ta bai wa Bayajidda su ne suka haifi ƴaƴayen da suka samar da Hausa Bakwai da Banza Bakwai.
Ɗan da Sarauniya Daurama ta haifa mai suna Bawo, shi ne ya haifi ƴaƴa Shida, shi kuma Ɗan da Gimbiya ƴar sarkin Borno ta haifa ya samar da ɗaya, kasancewar bayan da Bayajidda ya baro Borno ya shigo ta ƙasar haɗejia (Garin Gabasa) ne don haka ya bar Gimbiya Ƴar Sarkin Borno da Sarkin Borno ya aura masa a Haɗejia bai tafi da ita zuwa inda ya auri Sarauniya Darama ba.
SAMUWAR HAUSA BAKWAI
Ƴayan da Ɓawo ya haifa guda Shida ɗan gidan Sarauniya Darauma su ne suka Mulki:
Daura
Gobir
Kano
Katsina
Rano
Zazzau (Zaria)
Shi kuma Ɗan da Gibiya ƴar sarkin Borno ta haifa shi ne ya mulki:
Biram (wadda a yanzu take Haɗejiya, Jigawa).
Waɗanann garuruwa bakwai su ne suke jin Hausa tacacciya kuma ingantaciya a fuskar Hausawa.
SAMUWAR BANZA BAKWAI
A dai cikin tarihin Bayajiddan lokacin da ya kashe macijiyar nan a cikin rijiyar da take hana su ruwa sai mako-mako, sai ƴan garin suka nuna sha’awar su kan sarauniyasu ta auri Bayajidda ita kuma ta yarda aka yi aure da sharaɗin ba zai kwanta da ita ba saboda wasu dalilai, a saboda haka sai ta ba shi wata Baiwa mai suna Bagauriya, ita kuma Bagauriya sai ta haihu ta kuma sa masa suna Karp Da Gari Kokuma Karabagari.
Karabgari shi kuma ya haifi ƴaƴa Bakwai waɗanda su ne suka mulki waɗannan garuruwa na Banza Bakwai.
°Zamfara
°Kebbi
°Yawuri (Yauri)
°Gwari
°Kororafa (Kwararrafa, Jukun)
°Nupe, da,
Ilorin (Yoruba).
Su ma waɗannan Hausawa ne to amma a fuskar Hausa Bakwai ba su cika hausawa ba. Don haka suke kiran su Banza Bakwai.
Daga Mahmud Habibullah Taskar Nasaba,