yanzu yanzu muka Sami labarin nasarar jamian tsaro akan Yan tsadda
a yunkurin jamian tsaro na kawo qarshen taaddanci da fashi da makami a fadin jahohin Nigeria tayi gagarumin nasarar cika hannu da baragurbi cikin alumma
Rundunar Yan Sandan Jahar Adamawa tayi nasaran kama Yan Fashi da makami bayan da Suka kwache keke napep na wani bawan Allah.
Lamarin ya faru da sanyin safiyan yau Lahadi inda suka shiga keken a matsayin fasinjoji zuwa hayin gada. Ana chikin tafiya bayan sun hau gada se suka chiro makamai inda suka yiwa mai keken barazana har suka kwache keken.
Mai keke Napep din yayi maza inda ya shigar da korafi a ofishin Yan sanda na Jimeta Division wanda nan take aka kaddamar da farautan masu laifin har aka kamasu.
allah ya cigaba da tona masu asiri da duk masu daukar nauyinsu Ubangiji kasa mu gama lafiya Amin