Daga Muhammad Inuwa Zaria
Wani mahaifi ya aura yarinyar da dansa yake soyayya da ita, shidai wannan uba ya aura yarinyar da dansa yake sone sabo da shima Yana sonta.
A cewar uban wai yaron nasa bai isa aure bane shiyasa ya aureta, sabo da ya yaba da hankalin budurwan yaron nasa, sai dai ita yarinyar bata nuna tana son uban ba amma sai da uban ya nunama iyayen yarinyar kidi har ya aureta.
Sai dai yarinyar ta amince akayi auran Dan uban, ashe ta fake da haka ne don ta dunga ba shi saurayin nata hadin kai a dunga cin amanar mahaifin nashi har ta samu ciki.
Alokacin da uban ne yaga ta samu ciki shikuma uban ya shafama idonsa toka, yace a tafaf ba nasa bane cikin, ita kuma yarinyar tace nasa ne a yanzu dai magana tana kotu,
Wannan lamari ya farune mure dake cikin zamfara