Farashin Tumatur Ya Fadi Warwas a Najeriya
An samu faduwar farashin tumatur a kasuwanni da dama a Najeriya saboda shigo da shi daga wasu kasashe
An samu karancin tumatur a kwanakin baya sakamakon matsalar kwari da suka lalata gonakin tumatur
A baya ana siyan babban buhun tumatur N50,000 amma yanzu farashin ya fado zuwa N18,000 ko N20,000
Farashin kayan gwari musamman tumatur ya fadi a mafi yawan kasuwannin Najeriya sakamakon karin shigowa da shi daga kasashen Ghana da Cameroon.
Bincike ya bayyana yadda a baya aka samu karancin tumatur din a mafi yawan kasuwannin kasar sakamakon lalata shi da kwari su ka yi a mafi yawan gonakin tumatur a kasar.
Daily Trust ta tattaro cewa dilolin tumatur din sun yanke shawarar shigo da shi daga kasashen Ghana da Cameroon saboda maye gurbin wadanda aka rasa don yalwata shi a kasar.
Wadannan a cewar rahotanni na daya daga cikin dalilan da suka sa tumatur din farashin shi ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da kwanakin baya.
Binciken ya tabbatar da cewa baban buhun tumatur da a baya ake siyar da shi akan kudi N50,000, a yanzu ya sauko zuwa N18,000 zuwa N20,000 a jihar Kano saboda yawansa a kasuwanni.
Shugaban kungiyar masu noman tumatur (TOGAN) a jihar Kano, Alhaji Sani Danladi Ya da kwari ya bayyana cewa karancin tumatur da aka samu a baya bai rasa nasaba da kwari da suka lalata gonaki da yawa, yayin da ya ce shigo da tumatur din daga kasashe biyu a Nahiyar Afirka da kuma jihar Ogundaga Najeriya ya taimaka kwarai wurin faduwar farashin tumatur din a kasar.
“Mun shigo da karin tumatur daga jihar Ogun ta Najeriya, sannan da kuma kasashen Nahiyar Afirka guda biyu, Ghana da Cameroon, dilolin tumatur sun yi nasarar karya farashin tumatur din kuma yanzu ya yi yawa a kasuwanni yadda aka so.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim