Marcos Asensio zai bar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Marco Asensio ya ki amincewa da tayin karshe da aka yi na tsawaita kwantiraginsa a Real Madrid
Dan wasan Asensio, Zai bar Kungiyar ne a Matsayin wakili na kyauta kamar yadda yarjejeniyar kwantiraginsa za ta kare a karshen watan Yuni.
Dan wasan Ya kasance Koyaushe yana bai wa Real Madrid fifiko akan Dukkan Kulob amma kuma duk da Hakan an Gaza samun yarjejeniya kamar yadda abubuwa suke tare da yanke hukunci na ƙarshe nan ba da jimawa ba.
Amma ana Saran akwai yiyuwar Samu koma baya ba a maganar cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, amma idan Hakan Bai Samu ba abin ake sa rai shikenan dan wasan Asensio ya bar Kungiyar Ta Real Madrid da La Liga.
Manyan Kungiyoyin Premier League da kungiyar Kwallon Kafa Ta PSG Suna Daya Daga Cikin masu Niman dan Wasan Halin da ake ciki –
Cewar Wakilin Asensio Jorge Mendes.
Daga: Bashir Muhammad Maiwada