Yan sanda sun cafke dan acabar da yai wa Fasinjarsa Fy*de a Delta.
Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta kama Wani dan acaba Abdullahi Musa mai shekara 34 Da ya Yi wa fasinjar sa mai shekara 24 fyade.
Kakakin rundunar Bright Edafe wanda ya sanar da haka a Twitter ranar Laraba ya ce Musa ya yi lalata da yarinyar da karfin tsiya ta dubura.
Edafe ya ce Musa ya dauki wannan yarinyar ranar 28 ga Fabrairu a Asaba dai-dai ta sauka daga motar da ya dauko ta daga Benin jihar Edo.
“A wannan rana yarinyar ta iso Asaba cikin dare inda ta hau babur din Musa domin ya kai ta gida.
“Sai dai Musa bai kai ta gida ba yayin da suke hanya ya kutsa da ita wani daji ya danne ta a wurin.
“Yarinyar ta bayyana wa jami’an tsaro cewa Musa ya sadu da ita ta dubura ne saboda ya ga tana jinin haila. Ta Kuma ce ba ta yi ihu ba saboda ya yi barazanar zai kashe ta.
“Yarinyar ta ce Musa ya dauki hotunan tsiraicin ta kafin ya barta ta saka kayan ta sannan ya kwace turaren ta dake cikin jaka.
Edafe ya saka bidiyon Musa a yanar gizo ya na ba da labarin yadda ya yi wa yarinyar fyade da dalilin da ya sa ya sadu da ita ta dubura.
Zuwa yanzu rundunar ba ta da tabbacin ko Musa dan acaban gaske ne ko a’a.
Rundunar ta fara farautar Musa ranar biyar ga Mayu ta kuma kama shi ranar 20 ga Mayu.
Edafe ya gargadi mutane kan yin zirga-zirga da dare sannan su rika kula da irin mutanen da suke shiga ababen hawansu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim