Zan taka rawar gani na ganin APC ta riƙa yin Nasara a zaɓuka – Ganduje.
Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce zai taka rawa wajen tabbatar da nasarar jam’iyya mai mulki a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba 2023 a Imo, Kogi da Bayelsa.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin jawabin karbarsa a matsayin shugaban jam’iyyar bayan fitowar sa a taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa karo na 12 da aka gudanar a dakin taro na Congress Hall of Transcorp Hilton a Abuja.
Haka kuma NEC ta jam’iyyar ta zabi tsohon kakakin majalisar dattawa, Ajibola Basiru, daga jihar Osun a matsayin sakataren ta na kasa.
A cewar sa, za a samu daidaito tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Ganduje ya yi alkawarin zage damtse don ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabukan gwamnoni uku da ke tafe a Kogi, Imo da Bayelsa.
Jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi uku ne daga cikin jihohi takwas da ake gudanar da zabukan gwamnonin da ba a kakar wasa ta bana ba saboda kararraki da kuma shari’ar da kotu ta yanke a baya. Sauran sun hada da Anambra, Edo, Ekiti, Osun da Ondo.