Daga Usman Abubakar Kusfa.
Yadda aka tsinci wasu jarirai akan wata juji a safiyar yau Litini, jujin da ake kira da Kundin dake ‘Yan Tukaane Babban Dodon cikin garin Zariya.
Bugu da ƙari a yayin zantawar mu da wani ganau mai Suna Magaji Nepa, ya shaida mana cewa; yana cikin aikin ƙona bola sai yaga wata tsinma da alamun jini koda ya bude sai yaga jajirai inda nan take yakira al-umman wannan yaki inda aka sanar da hukuma da Mai Anguwan yankin.
Magaji Nepa yace koda suka ga jariran sun duba ba wanda ke motsi cikin su inda suka tabbatar basu da rai a lokacin, kuma jajiran tagwaye ne duka mata, inda nan take mai anguwa yabada umarnin ai masu sutura a birnesu, zuwa yanzu dai anmasu sutura an rufesu bisa ka’idan addinin Musulunci.