Na fara samun karancin Mu’amala da iyalina tun bayan cin zabena – Dikko Radda.
Tin daga lokacin da naci zabe na fara samun karancin lokacin da nake mu’amula da iyalina.
Zababben Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda, tin daga lokacin da yaci zabe ya fara samu karancin lokacin da yake Bacci, sannan ya samu ƙarancin lokacin da yake mu’amula da iyalinsa tin lokacin ne ya kara tabbatar da cewa aiki ne tuƙuru a jogaranci Gwamnatin jiha.
Sannan yayi ban hakuri game da wadanda suke ganin bai yi masu daide ba da kuma duk waɗanda suke bugo masa waya bain dauka ko kuma turo sako bai bada amsa su yi masa uzuri su yafe masa domin baida isasshen lokaci.
Don haka, ya kudiri aniyar yin aiki tukuru ga al’ummar jihar Katsina ne don tabbatar da cigaban jihar.
Ya kara da cewa, Idan shekara 4 ta cika al’ummar jihar Katsina suka ga sun masu daide su sake zaben su, idan kuma suka ga ba su yi ma su daide ba, suna da ra’ayin su zabi wasu su kuma sai su nade jikunansu su tafi Gida.
Dikko Radda ya bayyana haka ne yayin da yake tattauna wa da wakilin BBC a birnin Tarayya Abuja a lokacin da aka zaunar da Sabbin Gwamnoni domin sanar da su Sanin Makamar aiki a Abuja.
Yayi tuni da cewa, yana so mutane su san cewar kujerar Gwamna ba kujera ce ta wasa ba ko Sharholiya da kudaden Talakawa ba, yace yasan komai domin yayi shugaban ma’aikata na wasu watanni a ofishin Gwamnatin jihar Katsina duk ya san wainar da ake toyawa a wurin.