Kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji Captain Yahaya Ibrahim a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sunyi wani shiri ne a ranar Alhamis din da ta gabata a kauyukan Dada, Rukudawa, da Dumburum a karamar hukumar ZURMI ta jihar ZAMFARA.
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Yamma ta (Operation Hadarin Daji) a yunkurinsu na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi a lokacin bukukuwan karshen shekara, sun zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addan, yayin da sojojin suka lalata sansanonin ‘yan bindiga, inda suka kashe biyar (5) daga cikinsu tare da kwato makamai da alburusai a jihohin Zamfara da Sokoto.
Ya ce a yayin farmakin an yi arangama tsakanin sojojin da ‘yan bindigar inda sojoji suka yi kaca-kaca da ‘yan bindigar sannan kuma karfin sojojin ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya da gudu da raunukan harbin bindiga.
“Bugu da kari, sojojin sun ci gaba da zafafa hare-haren tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga Gwaska Dan Karami da Dangote wadanda suka bar maboyarsu suka tsere cikin rudani,” in ji shi.
“A wani samame sojojin sun kwato bindigogin guda biyu, Babura biyu, kakin soja guda shida daban-daban, na’urorin sadarwa, da alburusai.”
A wani samame da rundunar hadin guiwa ta Operation Hadarin Daji da ke jihar Sokoto suka yi a wani samame da suka kai sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda hudu a kauyen Masasa na jihar.
Kakakin ya kara da cewa “A yayin arangamar, ‘yan ta’adda da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka kwato bindiga kirar AK-47 daya, Wayar Tecno guda biyu, da kudi N282,050,” in ji kakakin.