Ana ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro a Abuja, na baya-bayan nan dai shi ne harin da aka kai wani gida mai tazarar mita 200 kusa da sansanin sojoji dake Pambara a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
A yayin harin, an yi garkuwa da wani Aondo Ver, wanda aka ce darakta ne a Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya.
‘Yan bindigan sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis, Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun samu shiga ta katangar.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, rundunar sojin ba ta ce uffan ba kan lamarin.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wasu ‘yan bindiga sun shiga wani gida a unguwar Guita, Chikakore, Kubwa, karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja, suka yi garkuwa da wasu ‘yan uwa mata biyu.
Aminiya ta ruwaito cewa, garkuwa da mutane da a baya an takaita shi ne a yankin Arewa maso Yamma, a ‘yan watannin nan ya yadu zuwa jihohi da dama da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Daga Zubaida Ali Taraba