Wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Godsgift Uweghwerhen a ranar Larabar da ta gabata ya yi wa ɗiyarsa mai shekaru uku bulala har lahira a unguwar Aladja da ke karamar hukumar Udu a jihar Delta.
ALFIJIR HAUSA, ta samu labarin cewa wanda ake zargin ya gudu ne bayan faruwar lamarin.
Sai dai jami’an Ƴan banga na Aladja a unguwar Ubogo ne suka kama shi, aka mika shi ga Ƴan sanda a sashin Ovwian/Aladja.
An bayyana cewa mutumin ya kashe yarinyar ce saboda ta shiga gidan makwabcinsa.
Ya yi mata bulala tare da raunata ta wanda hakan yasa ta jima tana jinya kana tarasu daga baya.
Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, a wani sako da ya aika wa wakilinmu a Warri, a safiyar ranar Alhamis, ya ce, “sun tabbatar” tare da bayar da cikakken bayani daga bangaren ƴan sandan ba.
Rahoto: Sahmsu S Abubakar Mairiga .