Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai kayar da abokan hamayyarsa a zaben 2023 kamar yadda Arsenal ta yi nasara a kan Chelsea a gasar Firimiyar Ingila.
Arsenal ta koma saman teburin gasar Firimiyar Ingila bayan da ta doke Chelsea da ci 1-0 a Stamford Bridge ranar Lahadi bayan da Gabriel ya ci.
Yayin da yake taya “Gunners” murna, tsohon mataimakin shugaban ƙasar wanda kuma masoyin Arsenal ne ya yi alkawarin yin haka ga ‘yan Najeriya a zaɓen shugaban kasa na watan Fabrairun 2023, bisani ya rubuta hakanne a shafinsa na Tuwita.