PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Tsohon Shugaban Jam’iyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC
Gwamna Yahaya Bello ya karbi dandazon mambobin PDP da suka sauya sheƙa zuwa.APC a karamar hukumar Igalamela/Odolu jihar Kogi
Wannan lamarin babbar barazana ce ga Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben da ke tafe a watan Nuwamba
Abdullahi Ibramin, tsohon shugaban rikon kwarya a karamar hukumar da wasu manyan jiga-jigai na cikin masu sauya sheƙar ranar Litinin
Dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi da ke tafe, Sanata Dino Melaye, na fuskantar babbar barazana ganain zaben wanda zai gudana a watan Nuwamba, 2023.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya tarbi tawagar gungun mambobin PDP daga karamar hukumar Igalamela/Odolu zuwa cikin jam’iyar APC ranar Litinin 22 ga watan Mayu.
Masu sauya shekar sun sha alwashin goyon bayan dan takarar gwamna a inuwar APC mai mulki, Ahmed Usman Ododo, kamar yadda jaridar Tribune Online ta rahoto.
Haka nan sun bayyana cewa zasu yi aiki tukuru ba dare ba rana domin tabbatar da APC ta ci gaba da mulkin jihar Kogi.
Tsohon shugaban PDP na rikon kwarya a karamar hukumar Igalamela/Odolu, tare da Honorabul Adama Sani da Aikoye Anu ne suka jagoranci masu sauya shekar daga gundumar Ajaka 1 da 2 zuwa APC.
A madadin tawagar masu sauya shekar, Ibrahim ya ce ayyukan Alherin da gwamna Bello ya zuba wa talakawa a kananan hukumomin Kogi ne suka ja hankalinsu zuwa APC.
RAHOTO -ZUBAIDA ALI TARABA