Shugaba Buhari ya bayyana cewa anci karo da cikas a cikin gwamantinsa.
Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ya Bayyana Nasarori 3 Da Aka Samu A Mulkinsa Tare da Cigaban Kasa.
Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a gaban Gwamnonin da ke barin mulki da masu jiran gado.
Shugaban Najeriya zai bar ofis nan da ‘yan kwanaki, ya nuna ya samu kalubale a gwamnatinsa.
Mai girma Buhari ya nuna inda aka ci karo da cikas da kuma wasu nasarori da gwamnati ta samu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tuna da shekaru kusan takwas da gwamnatinsa ta shafe a mulki, ya ce ba sumul abubuwa suka tafi ba.
Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna duk da kalubalen da aka samu, ya daura tubalin kawowa Najeriya cigaba, This Day ta fitar da wannan rahoton.
Shugaban kasar ya yi wannan magana ne da yake karanto jawabinsa a wajen taron da kungiyar gwamnoni na kasa ta NGF ta shirya a ranar Litinin a garin Abuja.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya karanto jawabin a madadin Mai girma Muhammadu Buhari ranar Litinin.
A jawabin da Farfesa Gambari ya karanto, ya ce gwamnatin tarayya ta samu nasarori daga 2015 zuwa yau, amma an ci karo da wasu kalubale a hanya.
Da yake ba kan shi maki, shugaban kasa mai jiran gado ya ce gwamnatinsa tayi abin a yaba ta fuskar gina abubuwan more rayuwa, noma da kuma tsaro.
“Mun yi ta samu cigaba daga lokacin da mu ka shiga ofis a 2015. Akwai gargada a hanyar saboda yanayin matsalar kudi.
Amma ina mai alfahari yayin da za mu bar mulki nan da makonni biyu cewa mun kafa tubali na kawo cigaba a Najeriya.
Ba za mu iya yin komai ba, amma mun maida hankali a bangarorin abubuwan more rayuwa, harkar gona da kara karfin soja.
Manyan da suka yi jawabi a wajen zaman da NGF ta shiryawa Gwamnoni masu jiran gado sun hada da Shugabar WTO watau Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.
Sun ta ce saura sun hada da Mataimakiyar shugabar majalisar dinkin Duniya, Amina Mohammed, Bukola Saraki, David Greene da kuma Tony Elemelu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.